Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Na Ci Gaba Da Kisan Mutane A Arewacin Najeriya


Shugaban Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu
Shugaban Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu

A Najeriya alamu na nuna cewa duk da matakan da wasu al'ummomi ke dauka don kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga, har yanzu tsugunne ba ta kare ba, domin mahara sama da dari biyar, dauke da muggan makamai sun afka wa kauyen Munhaye dake garin Bena a masarautar Zuru ta jihar Kebbi.

Maharan sun afka wa kauyen ne na Munhaye wanda yayi iyaka da jihohin Naija da Zamfara a wannan karshen mako misalin lokacin La'asar inda suka soma harbin kan mai uwa da wabi, abin da yayi sanadiyar salwantar rayuka da dama.

Mani John shi ne shugaban kungiyar ‘yan sa kai a yankin na Zuru ya ce yaransa sun kai dauki tare da sojoji amma dai sai da aka samu asarar rayuka.

Wakilin Sashen Hausa ya tuntubi wani mazaunin Bena, Salihu Muhammad Bena domin jin yanayin da ake ciki a kauyen bayan harin da aka kai.

Kafin wannan harin na kauyen Munhaye, wata hatsaniya ta so ta taso tsakanin Sojoji da ‘yansa kai wadanda jama'ar yankin ke kallo kamar wadanda suka karfin doka, inda ‘yansa kai suka je suka kewaye wurin sojojin a garin Wasagu.

Honorabul Sule Shindi shi ne shugaban karamar hukumar Danko Wasagu ya bayyana yanda lamarin ya faru.

Shugaban kungiyar ‘yansa kai, Mani John, ya ce sojojin abokan aikinsu ne kuma babu wata rigima tsakaninsu.

Wadannan abubuwan na zuwa ne lokacin da ‘yansa kai na yankin Zuru ke kawance da takwarorinsu na jihar Zamfara domin kare yankunansu daga ‘yan bindiga, duk da yake Fulani na yankin Zurun har yanzu suna ganin‘yan sa kan na saukar da haushi a kansu.

Ga cikakken rahoton Muhammad Nasir cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Karin bayani akan: Fulani, Zamfara, Sokoto, Nigeria, da Najeriya.

XS
SM
MD
LG