Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Miyagu Sun Yi Kisa Tare Da Sace Wasu Mutane a Jahar Nasarawa


Shugaban Yan Saandan Nigeria, Muhammaed Adamu Abubakar
Shugaban Yan Saandan Nigeria, Muhammaed Adamu Abubakar

A cigaba da aikata ta'asa da miyagu ke yi a fadin Najeriya, sun kai wani hari a Nasarawa, inda ake zargin sun sace mutane wajen ashirin, adadin da 'yan sanda ke tababa a kai.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani mutum suka kuma yi awon gaba da wasu mutane wadanda, ya zuwa yanzu, hukumomi ke tababa kan adadinsu.

Lamarin ya auku ne a yankin Gadabuke dake karamar hukumar Toto a jahar Nasarawa.

Shugaban karamar hukumar Toto, Prince Nuhu Adamu, ya ce bayanan da ya samu na nuna cewar ‘yan bindigar sun zo ne da yawan gaske, suka far ma ‘yan sintiri suka kashe mutum guda, sannan suka tasa keyar wasu zuwa daji suka yi garkuwa dasu.

Rundunar ‘yan sandan jahar Nasarawa, ta bakin kakakinta, Ramhan Nansel, ta tabbatar da mutuwar mutum guda amma ta kuma karyata rahotannin cewa mutane ishirin ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.

Yankin na Toto dai ya sha fama da ayyukan mahara da suka kashe mutane da dama, wasu dubbai suka kasance suna gudun hijira.

Ga ciakken rahoton Zainab Babaji ta sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG