Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Jinjina Ma Maharba a Adamawa Saboda Taimaka Masu


Maharba da Kayan Yakinsu.
Maharba da Kayan Yakinsu.

To a yayin da ake dada ganin rashin burgewar sojojin Najeriya saboda yadda miyagu ke cin karansu ba babbaka a fadin kasar, 'yan sadan sun yaba ma maharba da 'yan sa kai a jahar Adamawa saboda yadda su ka taimaka wajen yaki da miyagu.

A wani sabon mataki na zaburar da 'yan sakai na maharba da kuma 'yan Vigilante da yanzu ke taimaka wajen yaki da masu garkuwa da jama'a da sauran bata gari, rundunan yan sandan Najeriya ta soma Karrama wasu hazikan yan sakai da suka taimaka wajen cafke wasu masu garkuwa da jama'a a jihohin Adamawa da Taraba.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da matsalar ke neman gagaran kundila, musamman a jihohin arewa, inda kusan kullum sai ka ji miyagu sun aikata wata ta'asar tun ma ba a gama murmurewa daga wata ba.Ganin irin rawar da 'yan sa kai, musamman ma maharba, ke takawa wajen yaki da nau'ukan miyagu a sassa daban daban na kasar, musamman ma a shiyyar Adamawa, Kwamishinan 'yan sandan jahar, CP Olugbenga Adeyanju, da kansa ya jagoranci karrama 'yan sa kai da ke tallafawa wajen yaki da bata gari.

Kwamishinan yan sandan ya ce za su cigaba da hada kai da kungiyoyin sa kai na gari, ba yan tagaji ba.

To wai ko yaya wadanda aka karraman ke ji? Daya daga cikin kwamandojin yan sakai na maharban Adamu Galadima ya ce maharba sun taimaka sosai wajen kama masu sace mutane da sauran miyagu.

Baya ga maharba da yan sintiri na Vigilante haka nan rundunan yan sandan Najeriya ta Karrama wasu dake taimakawa kamar wannan bawan Allah da muka sakaya sunan sa sabili da tsaro.

Hajiya Aisha Bakari Gombi kwamandar mata a kungiyar maharban Najeriya
Hajiya Aisha Bakari Gombi kwamandar mata a kungiyar maharban Najeriya

Sau tari akan ci gajiyar ganga wanda daga bisani akan yada kwabren, inda ba kasafai gwamnatocin jihohi ke tunawa da rawar da yan sakan ke da shi ba.

Aisha Bakari Gombi da ke zama Sarauniyar Maharban Najeriya, na cikin wadanda ke sadaukar da rayukansu domin tallafa wa jami'an tsaro, inda ta ce sun yi tsayin daka wajen kare jama'a. To amma ta bayyana cewa su na fuskantar wasu matsaloli.

Ga Ibrahim Abdul'aziz da cikakken rahoton:

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG