Yayin da ake cigaba da zafafan muhawarori kan yawan satar mutane don neman kudin fansa, da sauran aika-aikar da miyagu ke yi a birane da kauyukan arewacin Najeriya, wadanda halaye ne da a baya ba a san Fulani da aikata su ba saboda tsabar fulaku, a yanzu wasu matasan Fulani, musamman ma wadanda aka raba su da shanunsu, sun wancakalar da Fulaku sun shiga irin wadannan miyagun ayyukan, al’amarin da ke bakanta ma magabatan Fulani rai.
Ba ma sai an fada ba, satar mutane don neman kudin fansa na neman zama (ko ma ya zama) sana’a a Najeriya, wanda da wuya a wayi gari ba tare da kaji an sace wani ba yallabai ba, musamman ma a arewacin kasar, inda ada labarin hakan ake ji a kudancin kasar.
Baya dai ga matsalar yan bindiga masu tada kayar baya irinsu Boko Haram, matsalar da ke biye yanzu haka ita ce ta tsaro, wadda ke cigaba da daure kai ganin matakan da hukumomin tsaro ke cewa su na daukawa kuma duk da ya ke masu fada a ji na daga cikin wadanda aka fai sacewa saboda ganin kitse da miyagun ke yi masu.
Ganin yadda ake yawan zargin matasan Fulani da sace mutanen, masu kokarin kare al’adar fulaku sun yinkuro don warware zare da abawa. Dr Aliyu Tilde wanda daya daga cikin shugabanin kungiyoyin fafutukar kare hakkin Fulani ne a Najeriya, ya danganta lamarin da tauye hakkin makiyaya da yawan sace musu shanu da aka tayi, al’amarin da ya raba matasan Fulani da sana’ar da su ka sani wato kiwo. Rashin sana’ar ya janyo fatara da yunwa, sannan ita kuma yunwar ta kori fulakun daga zukatan matasa masu karancin imani.
To amma Dr Tilde ya ce matasan Fulanin da ke aikata hakan sam ba su da hujjar yin haka. Abin da ya fi gare su shi ne rungumar sana’o’in da su ka dace da al’adar fulaku, wadda duk wani ba-Fullacen kwarai ke tinkaho da ita.
Shi ma da ya ke Karin haske Ambassada Hassan Jika Ardo, Jakadan Najeriya a yankin Trinidad da Tobego, wanda ma ke cikin shugabanin Fulani a Najeriya ya ce, yunkuri ne wasu ke yi domin bata zubar da kimar gwamnatin Najeriya a idon duniya.
Tuni dai wasu jahohi suka soma kafa dokar zartas da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da hannu a garkuwa da mutane.
Ga dai Ibrahim Abdul’aziz da cikakken rahoton:
Facebook Forum