Sanarwar fara yajin aikin kungiyar kwadagon dai ya sa gwamnatin jahar Kaduna kiran wani taron manema labaru inda ta ce ba za ta lamunci zanga-zangar da za ta lalata kayan more rayuwa na jahar ba. Kwamishinan Kananan hukumomi da masarautu na Jahar Kaduna Malam Ja'afaru Sani shi ya karanta wannan sanarwa.
Ya ce ya na so ya fadawa 'yan kwadago cewa wannan dokar ta hau kan kowa da kowa kuma har ma an riga an yi wa jami'an tsaro bayani kuma sun lashi takwobi cewa ba za su bari a bata dukiyar al'umma ba.
Sai dai kuma wannan barazana ba ta sauya tunanin kungiyar kwadagon ba saboda shugaban ta na Jahar Kaduna Kwamared Ayuba Magaji Suleman ya ce yajin aikin dai ba gudu ba ja da baya.
Karin bayani akan: NLC, Kaduna, zanga-zangar, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Tuni dai wasu daga cikin korarrun ma'aikatan Jahar Kaduna su ka fito don marawa wannan zanga-zanga baya.
Tun a yammachin jiya Lahadi dai gidajen mai su ka cika da motochi don tanajin mai yayin da mutane su ka dunga tsayawa bakin hanya ba motocin haya gidaje kuma sun yi dundum saboda ba wutar lantarki a fadin Jahar.
Saurari cikakken rahoton a sauti: