Karin farashin albarkatun man fetur kusan sau uku cikin shekaru hudu da gwamnati ta yi, tare da hauhawar kudin wutar lantarki, su ne manyan al’amuran da suka sanya kungiyar ta NLC ta ayyana ranar Litinin mai zuwa a matsayin ranar zanga-zangar lumana da kuma tsunduma yajin aikin gama-gari, domin matsawa gwamnati lamba ta sauya tunani.
Comrade Sa’idu Bello, tsohon Jami’in kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC ya ce da yana cikin shugabancin kungiyar a halin yanzu, da ba zai ba da goyon bayan shiga yajin aiki ba.
Bisa ga cewar Comrade Sa'idu, " lokacin da Buhari ya fito ya ce duk mutumin da ya shiga cikin gwamnati ya ce a sayar da litar man fetur akan Naira 45, to ya cuci ‘yan Najeriya. To amma yana hawa (mulki) ya kara (Farashin) zuwa Naira 145 amma talakawa suka yi shiru,” in ji Comrade Sa’idu Bello.
Sai dai yunkurin kungiyar kwadagon na gudanar da zanga-zangar da shiga yajin aiki ya hadu da cikas ne, bayan da wani lauya mai suna Sanusi Musa ya nemi kotu da ta dakatar da yunkurin na NLC, a madadin wata kungiya mai suna Incorporated Trustees Peace and Unity Ambassadors Association.
To amma duk da haka, Comrade Aliyu Gesto dake zaman tsohon sakataren kungiyar kwadago ta Najeriya reshen jihar Kano na cewa “gwamnati ta raina kungiyar kwadago, saboda ko ba komai tana ganin ita ce ta yi dokokin da take tafiyar dukkan harkokin a Najeriya har da dokokin da suka kafa kungiyoyin kwadago, saboda haka sun san lagon da za su kama su. Amma kuma duk yadda suke tsammani ba haka abin yake ba. Ina mai tabbatar maka cewa kungiyar kwadago idan za ta iya yin tsayin daka domin kwato wa talakan Najeriya ‘yancin sa, to babu mai iya hana su.”
A cikin shekara ta 2015, ana sayar da litar man fetur a najeriya akan naira 85 ne, amma a yanzu ‘yan kasar na sayan litar ne kan naira 160 zuwa sama.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Facebook Forum