Kungiyar kwadago ta Najeriya reshen jihar Kano ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin makonni biyu ta dawowa da ma’aikatan jihar kudaden da ta yanke musu a albashin su na watan Mayu ko kuma ta tsunduma yajin aiki na gargagadi.
Baya ga haka kungiyar ta bukaci gwamnati ta gaggauta gyara albashin ma’aikatan lafiya na kananan hukumomi da malaman makarantun firamare kana da ma’aikatan fannin shari’a na jihar domin ya yi daidai da kunshin yarjejeniyar aiwatar da tsarin mafi karancin albashi na dubu 30 da bangarorin biyu suka sanya wa hannu.
A yayin taron gaggawa da kungiyar ta NLC da sauran kungiyoyin kwadago suka yi a Kano, kungyar ta ce matakin na gwamnatin Kano ya ci karo da tanade-tanaden dokokin kwadago na Najeriya da kuma na kasa da kasa, a cewar Comrade Kabir Ado Minjibir shugaban kungiyar NLC a Kano wanda ya jagoranci taron,
Ya kuma ce sun yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta dawo da kudaden da ta yanka sannan kuma ta daina zaftare albashin, ta kuma ci gaba da biyan ma’aikata albashin dubu 30 kamar yadda aka saba.
Dangane da haka ne kungiyar ta ce babu shakka zata tsunduma yajin aiki na gargadi muddin gwamnati ta gaza daukar matakan da suka dace cikin makonni biyu masu zuwa.
Sai dai kwamishinan kudi na jihar Kano Alhaji Shehu Na-Allah, wanda ma’aikatarsa ce ke kula da harkokin albashin ma’aikata ya ce gwamnati na kishin al’umma da ma’aikata, kudaden da ke shigowa sun yi kasa, shi ya sa ta yi amfani da kudaden da ta ke da su ganin cewa ba jihar ce kadai ke fuskantar matsalar tattalin arziki ba.
Gabanin wannan wa’adi na ‘yan kwadago, akwai zargin cewa magabatan kungiyar NLC da gwamnati bakin su daya.
Shugaban kungiyar kwadago ta jihar Kano Comrade Kabiru Ado Minjibir, ya kalubalanci duk wani jami’i da ya kawo wata takarda ko wani sakamako na taro da aka yi wanda ya samu yarjejeniyar ma’aikatan kwadago na jihar akan a yanki albashin ma’aiktan jihar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti daga wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari:
Facebook Forum