Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Kwadago NLC da TUC Sun Yi Barazanar Fara Yajin Aiki


Zanga Zangar NLC
Zanga Zangar NLC

Gamayyar kungiyoyin kwadago ta NLC da TUC sun yi barazanar fara yajin aikin gamagari a ranar Litinin 28 ga watan Satumba.

Tun bayan cire tallafin man fetur da kari a kan farashin wutan lantarki a ke cigaba da kai ruwa rana tsakanin kungiyoyin kwadagon Najeriya, yan kasar da gwamnati inda aka yi ta tattaunawa a kan janye matakin domin rage radadin da marasa karfi ke ji, sai dai haka bata cimma ruwa ba. Ganin haka gamayyar kungiyoyin kwadagon kasar ta yi barazanar fara yajin aikin gamagari har sai gwamnati ta dauki matakin “sausautawa talaka”.

A cikin hirarshi da Muryar Amurka, mataimakin sakataren kungiyar kwadagon Najeriya -NLC, Kwamarade Nasiru Kabir ya bayyana cewa, sun sha zama da gwamnatin tarayya a kan batutuwa da yawa ba wannan batun kadai ba, da ya hada da matsanancin kuncin rayuwa da ma’aikatan Najeriya da kuma talakawa su ke ciki sai dai I zuwa yanzu, babu alamar ci gaba.

likitoci-sun-fara-yajin-aiki-a-najeriya

kungiyar-kwadagon-jihar-kano-ta-yi-barazanar-fara-yajin-aiki

ba-gudu-ba-ja-da-baya---asuu

Kwamrade Nasiru ya ce suna kan wannan tattaunawar ne suka wayi gari gwamnati ta janye tallafin man fetir ta kuma kara kudin wutar lantarki, abinda yace ma’aikatan ba zasu lamunta ba.

Zanga Zangar NLC 2017
Zanga Zangar NLC 2017

Kungiyoyin kwadagon NLC da TUC dai sun ci alwashin hada gwiwa da sauran mambobin su a duk fadin kasar tare da neman goyon bayan sauran ‘yan Najeriya domin ganin yajin aikin ya yi tasiri.

Da yake maida martanin dangane da barazanar yajin aikin, mataimakin shugaban kasa na musamman a kan sha’anin yada labarai, Mallam Garba Shehu, ya bayyana cewa, abinda ya kawo jinkiri a ba kungiyar kwadago amsa dangane da bukatar da ta gabatar shine, kokari da ake yi na ganin ministoci sun dauki matsaya daya,

Bisa ga cewarsa, “dole ce ta sa gwamnati ta janye tallafin man fetir domin tana fuskantar koma bayan tattalin arziki sakamakon bullar annobar Coronavirus” Ya kara da cewa, “kudin shiga da Najeriya ta ke samu ya fadi da kashi sittin da shida cikin dari”. Dangane kuma da wutar lantarki, Garba Shehu ya ce “ana bada wuta ta Naira biliyan arba’in da biyar amma kamfanoni masu zaman kansu da suke samar da wutar lantarkin biliyan goma sha byar kadai suke kawowa, sauran gwamnati ke cikawa.”

Zanga Zangar NLC 2017
Zanga Zangar NLC 2017

Idan ba a manta ba, gwamnatin tarayyar da kungiyoyin kwadagon sun gana kimanin makonni biyu da suka gabata amma ba a cimma matsaya ba saboda gwamnatin ba ta amince za ta janye karin kudin ba ko kuma bawa mutane tallafi musamman ma'aikata

Yau alhamis ne ake kyautata zaton gwamnatin tarayya zata gana da hadakar kungiyoyin kwadago ta Najeriya da nufin dakile shiga yajin aikin.

Saurari rahoton Halima Abdulra’uf cikin sauti:

Kungiyoyin Kwadago NLC da TUC Sun Yi Barazanar Fara Yajin Aiki-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG