Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yanzu Babu Ruwana Da Siyasar Jam’iyya – Obasanjo


Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo (Instagram/ Olusegun obasanjo)
Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo (Instagram/ Olusegun obasanjo)

“A irin duniyar da nake rayuwa, idan ka ce sai da safe, ba ka sake komawa ka ce ina wuni." In ji Obasanjo.

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, ya nesanta kansa da wasu rahotanni da ke cewa yana shirin kafa sabuwar jam’iyya gabanin zaben 2023.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, ta hannun kakakinsa Kehinde Akinyemi, Obasanjo, wanda yanzu haka yake kasar Afghanista bisa gayyatar Shugaba Ashraf Ghani, ya ce rahoton da aka wallafa a jaridar Vanguard wanda ke nuna cewa ya zabi wasu tsoffin gwamnoni uku a matsayin mataimakansa wajen kafa jam’iyyar, ba gaskiya ba ne.

“Wannan rahoto ba shi da tushe balle makama, babu wani shiri na kafa wata sabuwar jam’iyya a yanzu ko a nan gaba.” In ji Obasanjo.

Sanarwar ta kara da cewa, tsohon shugaban na Najeriya ya lura cewa wasu suna so su tsoma shi a cikin rikita-rikitar siyasa.

“A irin duniyar da nake rayuwa, idan ka ce sai da safe, ba ka sake komawa ka ce ina wuni.

“Na gama da siyasar jam’iyya, amma lura da matsayin da nake da shi a Najeriya da Afirka, kofata a bude take ga duk wani ko wata kungiya da ke son jin ra’ayina ko neman shawarata, kuma zan ba su daidai iya yadda zan iya, ba tare da na kasance mamba a wannan kungiya ba.”

A cewar tsohon shugaban kasar, jam’iyyarsa ita ce ta ‘yan Najeriya da ke fuskantar matsalolin tsaro, rashin aikin yi, yunwa, talauci da sauran kalubale, yana mai jaddada cewa jam’iyyarsa ita ce, wacce za a ceto Najeriya don ta ci gaba da zama a matsayin kasa daya cikin kwanciyar hankali, tsaro, adalci da ci gaba.

“Ya kamata wadanda suke kokarin bullowa ta baya don su tilasta Cif Obasanjo ya koma siyasar jam’iyya, su mutunta zabin da ya yi na zama ba tare da jam’iyya ba”

Obasanjo ya mulki Najeriya a tsakanin 1999 zuwa 2007 karkashin Jam’iyyar PDP.


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG