Karamar Ministar kula da masana’antu da harkokin cinikayya ta Najeriya Maryam Yalwaji Katagum ta yanki jiki ta fadi yayin da take shirin gabatar da jawabi a wani taron kaddamar da wani shirin bunkasa tattalin arziki.
Lamarin ya faru ne a jihar Bauchi inda ministar ta je don kaddamar da shirin wanda aka yi Sanin Malam Plaza da ke kan hanyar Ahmadu Bello.
Rahotannin sun ce nan take aka garzaya da ita asibitin horarwa na ATBU don ba ta taimakon gaggawa.
Taron da lamarin ya faru ya samu halartar mataimakin gwamnan jihar ta Bauchi Sanata Baba Tela.
Karin bayani akan: Ahmadu Bello, jihar Bauchi, Daily Trust, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ministar wacce ‘yar asalin jihar Bauchi ce ta isa garin tun a ranar Asabar.
A baya-bayan nan, Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an dauke ministar daga sashen kula wadanda suka shiga dimuwa an mayar da ita daki na musamman bayan da ta farfado kuma bayanai sun yi nuni da cewa matsalar da ta samu ba ta yi muni ba.
A watan Yulin 2019, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Katagum a matsayin karamar ministar kula da masana’antu.