Buhari ya yi wannan kira ne cikin wata sanawar da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Litinin, inda shugaban ya kuma nuna damuwarsa kan yawan hare-hare da ake kai wa jihohin Kaduna da Neja, wadanda suke karewa a kan dalibai.
“Duk da cewa ana samun ci gaba wajen tura karin jami’an tsaro zuwa yankunan da ke fama da rikicin, shugaban ya nemi jami’an tsaro da su hanzarta kubutar da dukkan dalibai maza da mata a wadannan yankuna tare da tabbatar da sun koma gida lafiya.” Sanarwar ta ce.
Karin bayani akan: Garba Shehu, Neja, Kaduna, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Shugaban kasar ya kara da cewa, matsalar garkuwa da dalibai, wacce ke yawan faruwa a arewacin Najeriya, na maida hannun agogo baya wajen zuwan yara makaranta a jihohin da da ma suke baya-baya wajen samun ilimi.
“Shugaba Muhammadu Buhari, ya kwatanta ayyukan garkuwa da mutane a matsayin ragwanci da abin kyama, yana mai Allah wadai da lamarin, wanda yake shafar iyalai da kasa baki daya.