NAHCON ta ce ya zama wajibi a samu bayanai na bai daya ga maniyyata don ba su kwarin gwiwar cewa da yardar Allah za a cimma burin sauke faralin.
Shugaban hukumar Zikrullah Kunle Hassan ya ce duk da rashin zuwa hajjin, hukumar na ci gaba da tsare-tsare kan yadda za a tunkari zuwa hajjin da zarar an bude dama don amfanin dubban maniyyata daga Najeriya.
Kunle Hassan wanda a shekarar da ya hau mukamin jagorancin hukumar duniya ta fada kalubalen coronavirus, ya ce wajibi ne hukumar ta rika samar da bayanai ga maniyata don zama cikin shirin gujewa fafe gora ranar tafiya.
Mahalarta taron sun bayyana irin tambayoyin da suke samu daga maniyyata kan aikin hajjin da yake cikin runkunan Musulunci biyar.
Karin bayani akan: Dr. Aliyu Tanko, NAHCON, Saudiyya, Nigeria, da Najeriya.
A gefe guda hukumar ta na kara inganta shirin adanar kudi don samun gudanar da aikin hajji ta hanyar ajiyar kudi na tsawon lokacin da maniyyaci zai iya tara kudin kujera.
Kamar yadda shugaban sashen Dr. Aliyu Tanko ya fada, tsarin tamkar wanda a ke yi ne a Malaysia inda mai niyya zai yi ta tara kudi har ya samu damar akalla ya je hajji a rayuwarsa sau daya.
NAHCON da a ka kafa a 2006 daga sashe a ma'aikatar waje, kan zama mai shiga yarjejeniya a madadin jihohi kan aikin hajji da Saudiyya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Hauwa Umar:
Hukumomin Saudiyya Sun Shirya Karban Alhazai a Mina