Ma’aikatar tsaron jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar mutuwar sojojinta 10 a wani karo da ya hada su da ‘yan bindiga a yammacin kasar.
Lamarin ya faru ne a yammacin Litinin 3 ga watan Fabrairun 2025 lokacin da aka kira dakarun tsaro masu sansani a Bankilare zuwa kauyen Takourzat na jihar Tilabery inda wasu barayi suka kore garken dabobi, a yayin da askarawan suka bi sawun wadanan barayi sun fada tarkon ‘yan bindiga a wani wurin da suka yi kwanton bauna abin da ya haddasa rasuwar sojoji 10 inji ma’aikatar tsaron.
Ma'aikatar ta kara da cewa duk da daukin da aka aike ta sama da kasa ba a yi nasarar cafke maharan ba sakamakon yadda suka fantsama cikin daji.
To amma matakin da aka dauka a washegari don zuba ido ta sama ya ba da damar fatattakar ‘yan ta’addar lokacin da suka taru a wani wuri kamar yadda suka saba a duk lokacin da suka yi aika-aika.
An kashe kalla 15 daga cikinsu tare da raunata da dama inji sanarwar. Sun kuma yi kiran gwamnatin ta Nijer da al’ummar kasar a kan maganar kara tsaurara matakai.
Nijar wacce ke fama da barnar ‘yan ta’addan yankin Sahel da na Boko Haram na da hadin gwiwa a fannin tsaro da makwabtanta Mali da Burkina Faso.
Ga matakan cikin gida inda a karshen watan Janairun da ya gabata da farkon watan nan na Fabrairu aka yaye sabbin sojoji kusan 3000 a cibiyar horon soja da ke jihar Zinder da wacce ke kwaryar birnin Yamai.
Ministan tsaron kasa janar Salifou Mody a wata hira da manema labarai a baya bayan nan ya sha alwashin magance matsalolin tsaron da ake fuskanta ta hanyar sauye-sauyen da aka aiwatarwa daga 26 ga watan Yulin 2023 kawo yau.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna