Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-Haren Ta'addanci Sun Yi Sanadin Rasuwar Sojoji Da Farar Hula A Jihar Tilabery


Yan bindiga
Yan bindiga

Lamarin ya faru ne da la’asar ta ranar Litinin 20 ga watan Mayun 2024 lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai harin ta’addanci kan sansanin soja a kauyen Boni na gundumar Makalondi da ke tsakanin iyakar Nijer da Burkina Faso.

Hukumomin jamhuriyar Nijar sun sanar cewa dakarun kasar sun hallaka gomman ‘yan ta’adda a kauyen Bony da ke gudumar Makalondi a Jihar Tilabery yayin da sojoji 7 suka rasu a sakamakon wani harin da aka kai a ranar litinin din da ta gabata.

Sojojin Nijar
Sojojin Nijar

Lamarin da ya sa kungiyar hadin kan al’ummar jihar Tilabery nanata kiran hukumomi su kara jan damara ganin yadda a dai dai lokacin da ake alhinin abubuwan da suka wakana a kauyen Bony wasu ‘yan bindiga suka hallaka fararen hular a kauyen Djambala na karamar hukumar Sakoira shi ma a jihar ta Tilabery.

Lamarin ya faru ne da la’asar ta ranar Litinin 20 ga watan Mayun 2024 lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai harin ta’addanci kan sansanin soja a kauyen Boni na gundumar Makalondi a iyakar Nijar da Burkina Faso.

Sanarwar da ma’aikatar tsaron kasa ta bayar kenan a kafafen gwamnati inda ta ke cewa askarawa 7 su ka rasu sannan mutun 2 sun jikkata 1 daga cikinsu farar hula an kuma yi asarar motoci 4 yayin da sojoji suka yi nasarar kashe gomman ‘yan ta’adda an kuma kona masu ababen hawa.

Tuni aka baza dakarun sama da na kasa don farautar wadanan mahara da suka ranta a ta kare.

Shugaban kungiyar hadin kan al’ummar Tilabery Comite union Tilabery Amdaou Harouna Maiga ya bayyana damuwa kan yadda matsalar tsaro ta ki ci ta ki cinyewa a wannan yanki mai makwaftaka da kasashen Mali da Burkina Faso.

A dai dai lokacin da ake juyayin faruwar wannan al’amari wasu ‘yan bindigar na daban sun afkawa jama’a a kauyen Djambala na karamar hukumar Sakoira inda suka yi awon gaba da garken dabbobi.

Faruwar haka ya sanya matasan kauyen bin sawun barayin da zummar kwato dabbobin sai dai sun fada tarkon barayin a wani wurin da suka yi kwanton bauna.

Ya zuwa yanzu ba wani bayani a hukumance dangane da abinda ya wakana a Djambala yayin da masu amfani da kaffafen sada zumunta ke tafka mahawwara a kai.

Saurari rahoton :

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG