Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Mashigar Birnin Yamai


Jami'an Tsaron Jamhuriyar Nijar
Jami'an Tsaron Jamhuriyar Nijar

Isowar su tashar binciken ke da wuya suka shiga bude wuta.

A jamhuriyar Nijar ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne sun kai hari a daren ranar Alhamis a wata tashar bincike ta jami’an tsaron jandarma da ke da tazarar kilomita 13 daga birnin Yamai kan hanyar garin Say.

Kawo yanzu ba bayanai a hukumance, sai dai wasu majiyoyi sun tabbatar da rasuwar mutane a sakamakon wannan al’amari da ya wakana a wani lokacin da rahotanni ke cewa an gwabza fada tsakanin ‘yan kato da gora da ‘yan bindiga a wani kauyen jihar Tilabery da ke iyaka da Burkina Faso.

A wajen karfe 8 da rabi na daren ranar Alhamis ne maharan, da suka zo cikin motoci 2 kirar Hilux, suka afkawa tashar bincike ta jami’an tsaro da ke kauyen Laoudou mai tazarar kilomita 13 kan hanyar Say, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fararen hula 3, a cewar wata majiyar da ba ta hukuma ba.

Dr Bounty Diallo, masani akan sha’anin tsaro kuma mazaunin gundumar Yamai ta 5, wato shiyyar da ke makwabtaka da kauyen da abin ya faru, ya tabbatar da cewa wasu ‘yan ta’adda sun kawo hari tashar binciken jami’an tsaron jandarma.

Kawo lokacin hada wannan rahoto ba wasu bayanai a hukumance, to amma wani rahoton majiyar tsaro ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kuma kara da cewa maharan su kimanin 20 sun fito ne daga wajen garin Say cikin motoci 2 inda suka lullube kansu da tamfol da nufin badda kama.

Isowar su tashar binciken ke da wuya suka shiga bude wuta.

Jandarmomi sun maida kakkausan martani, sai dai hakan bai hana wa ‘yan ta’addan tserewa da motoci uku ba, cikin su daya ta hukumar jandarma da bindiga AK-47 guda daya. Sannan mutane uku sun mutu, dukkansu farar hula yayin da jandarmomi biyu suka ji rauni wadanda aka kwantar a asibiti.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan kisan da ‘yan bindiga suka yi wa wani malamin makaranta a kauyen Bakanta na gundumar Makalondi a jihar Tilabery.

Cherif Issofou shine babban sakataren kungiyar malaman kwantaragi ta SYNACEB, ya ce tun da farko ‘yan bindigar sun sace malaman makaranta biyu, inda daga bisani suka dawo da su inda suka kashe daya kuma suka saki daya.

Wani al’amarin mai nasaba da sha’anin tsaro shine wanda ya wakana a kauyen Tchalkam na karamar hukumar Torodi mai tazarar kilomita 20 da garin Samira a ranar Laraba, inda aka yi arangama a tsakanin ‘yan sa kai da ‘yan bindiga.

Matsalolin tsaro a yankin Sahel wani abu ne da ake magani kai ya na kaba.

Tsanantar al’amarin ne ma yasa sojoji a kasashe 3 da abin ya addaba wato Mali da Burkina Faso da Nijar su ka yi juyin mulki da nufin samo mafitar abin, sai dai kuma dukkan kokarin da aka sa gaba a cikin gida ko a karkashin inuwar kungiyar da aka kafa ta AES ana iya cewa har yanzu da sauran rina.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

NIJAR: 'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Mashigar BirninYamai.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG