Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NIJAR: 'Yan Bindiga Sun Sako Wasu Sojojin Da Suka Kama A Harin Tilabery


Nijar - 'Yan bindiga sun sako wasu sojojin da suka cafke
Nijar - 'Yan bindiga sun sako wasu sojojin da suka cafke

Wasu ‘yan kasar ta Nijar ne a karkashin wani kwamiti mai zaman kansa suka shiga tsakani har aka cimma nasarar kubutar da wadanan sojoji da tuni suka gana da shugaban gwamnatin mulkin soja Janar Abdourahamane Tiani a yammacin a ranar Alhamis.

'Yan bindiga sun saki sojojin da suka cafke a yayin harin da aka kai wa jami’an tsaro a watan Mayun da ta gabata a kauyen Boni dake jihar Tilabery iyaka da Burkina Faso.

Nijar - Lokacin wani taro na duba sojojin da 'yan bindiga suka sako
Nijar - Lokacin wani taro na duba sojojin da 'yan bindiga suka sako

A ranar 20 ga watan Mayun 2024 ne ‘yan bindiga suka afka wa wata tashar jami’an tsaro a kauyen Boni na karamar hukumar Makalondi inda aka yi gurmuzu sosai lamarin da yi sanadin mutuwar sojoji 7 da ‘yan bindigan da ba a bayyana adadinsu ba sai dai maharan sun yi nasarar awon gaba da sojoji 6 wadanda kwanaki kadan bayan haka suka bayyana a wata bidiyon da aka nada a wurin da aka yi garkuwa da su.

Hakan ne ya sa wani kwamiti mai zaman kansa mai kunshe da ‘yan Nijar zalla yunkurin shiga tsakani ta yadda za a karbo wadanan dakaru ta hanyar sulhu.

Shugaban kungiyar makiyayan arewacin jihar Tilabery Boubacar Diallo na daga cikin wadanda suka yi wannan aiki.

Tuni wadannan sojoji su kimanin 6 da mutanen da suka yi aikin shiga tsakani suka gana da shugaban majalissar CNSP Janar Abdourahamane Tiani da mukarrabansa.

'Yan bindiga sun sako wasu sojojin da suka cafke a Nijar
'Yan bindiga sun sako wasu sojojin da suka cafke a Nijar

Fira minista Ali Lamine Zeine da ke bayani dangane da wannan al’amari amadadin hukumomin kasar ya yi godiya da jinjina ga wadanda suka yi wannan aiki sannan ya bayyana cewa "‘yan Nijar dukkansu daya suke duk duniya ta shaida mutane ne masu soon zaman lafiya. Dukkan ‘yan kasa hatta wadanda suka dauki makamai su hamzarta su dawo gida domin mu gina kasarmu tare. Ba mu da wata kasa sai ita kuma abubuwan da suka faru a yanzu na nuna cewa wannan ita ce hanyar da ya kamata dukkanmu mu bi wajen tafiyar da lamura."

Kashe wutar rikici ta hanyar sulhu dadaddiyar dabara ce da aka yi amannar cewa ita ce mafi a’ala wajen warware kowace irin takaddama kamar yadda masana suka sha nanata bukatar bin hanyoyin da ba na karfi ba wajen magance matsalolin tsaron da ake fama da su a kasashen sahel a cewar Abdourahamane Alakssoum mai sharhi kan al’amuran yau da kullum.

Tuntubar ‘yan bindiga akan maganar sulhu wani mataki ne da aka ayyana cewa ya taimaka sosai wajen lafawar hare haren ‘yan bindiga da na ‘yan ta’adda a zamanin hambararriyar gwamnatin Mohamed Bazoum.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

NIJAR: 'Yan Bindiga Sun Sako Wasu Sojojin Da Suka Kama A Harin Tilabery
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG