Koda yake an yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda fiye da 30 kamar yadda hukumomin tsaron kasar suka bayyana a wata sanarwa.
Labarin wannan hari da aka ayyana a matsayin mai cike da sarkakiya ya fara bayyana ne a jiya Alhamis da rana a kafafen sada zumunta inda wasu majiyoyi suka sanar cewa, an yi babban gumurzu a tsakanin sojojin Nijar da wasu ‘yan bindigar da suka yi kwanton bauna a kewayen kauyen Teguey na gundumar Bankilare dake jihar Tilabery gab da iyakar kasar da kasashen Mali da Burkina Faso.
Majiyar ta bayyana cewa, a sakamakon wannan al’amari sojoji 21 sun rasu wasu 34 sun yi batan dabo yayinda wasu 27 suka ji rauni tare da lalata motoci masu silke 5 da wasu motoci 4 koda yake majiyar ba ta yi bayanin komai ba dangane da abinda ya faru da ‘yan ta’adda da suka kitsa wannan hari.
To amma hukumomin tsaro a sanarwar da suka bayar a kafar talbijan mallakar gwammnati a cikin daren jiya Alhamis labarin ya sha bamban suna masu cewa, ‘yan bindiga sama da 100 sun kai harin kwanton bauna mai cike da sarkakiya kan sojojin Nijar a tsakanin kauyen Teugey da Bankilare. Maharan sun yi amfani ne da boma-boman gargajiya da suka haka a jikin motoci tare da bizne wasu kan hanya.
Dakarun wannan kasa sun maida kakkausan martani kan ‘yan ta’addan da suka zo kan Babura da motoci. An yi gumurzu sosai inda sojoji suka hallaka abokan gaba fiye da 30 koda yake askarawa 23 sun rasu wasu 17 da suka ji rauni na samun kulawa a asibiti yayin da aka lalata wasu motoci na yaki 4 da wasu pick-up 4 a cewar sanarwar ma’aikatar tsaron kasa.
Mahukunta da sunan Shugaban Majalissar CNSP sun yaba wa jami’an tsaron Nijar game da abinda suka kira jajircewarsu akan maganar tabbatar da tsaro da kare martabar kasa , suna masu jaddada kara jan damar domin ci gaba da ayyukan murkushe ayyukan ta’addanci don samar da tsaro da kwanciyar hankali a kasa.
Jamhuriyar Nijar makwaciya ga Mali da Burkina Faso na fuskantar matsalolin tsaro a yankin Tilabery sakamakon yaduwar aika aikar ‘yan ta’addan da suka addabi kasar Mali yau shekaru sama da 10.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna