Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar, Burkina Faso, Mali Sun Daura Damarar Yaki Da Ta'addanci


Shugabannin mulkin soja na kasashen Burkina Faso, Nijar da Mali
Shugabannin mulkin soja na kasashen Burkina Faso, Nijar da Mali

A cewar Ministan tsaron Nijar, an tanadi motoci da jirage da makaman yaki sannan hafsoshin kasashen uku na tattaunawa da juna kuma tuni suka kammala tsara yadda ayyukan rundunar za su gudana.

Runudunar hadin gwiwar kasashen AES, Nijar, Mali da Burkina Faso mai dakaru 5,000 na shirin fara ayyukanta nan da 'yan makwanni masu zuwa a ci gaba da jan damarar yaki da kungiyoyin ta'addancin da suka addabi yankin Sahel shekaru sama da 10.

Ministan tsaron Jamhuriyar Nijar, Janar Salifou Mody, ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman.

A yayin da yake bitar sha’anin tsaro watanni 18 bayan juyin mulkin soja, Minista Mody, ya fara da tunatarwa game da halin da ake ciki kafin ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Ya na cewa a wancan lokaci sha’anin tsaro abu ne da aka sakar wa wasu dillalan cikin gida da dillalan kasashen waje musamman sojan Faransa.

Bayan raba gari da dakarun Faransa wasu kasashen sun zabi ficewa daga Nijar inda aka yi rabuwa ta hanyar diflomasiya in ji shi.

Dalilin da kenan shekarar 2024 ta kasance wajen mayar da hankali kan sake fasalta tsarin ayyukan rundunar tsaron kasa tare da samar da karin sojoji da matsa kaimi a ayyukan ba da horo da samar da kayayakin yaki.

Sabbin jami’ai manya da kanana kusan 13,000 ne aka dauka a bara. Abin da ke ba da damar girke asakarawa 18,000 a kowace rana a fadin kasa.

Sai dai wani mai adawa da gwamnatin mulkin sojan ta Nijar, Siradji Issa, na nuna rashin gamsuwa da halin da ake ciki a yau a wannan fanni.

Dangane da rundunar hadin gwiwar da kasashen Sahel suka ba da sanarwar kafawa a bara, Mody ya ce rundunar mai sojoji 5,000 za ta fara aiki nan da ‘yan makwannin da ke tafe.

A cewarsa, an tanadi motoci da jirage da makaman yaki sannan hafsoshin kasashen uku na tattaunawa da juna kuma tuni suka kammala tsara yadda ayyukan rundunar za su gudana.

Sai dai masana na gargadi kan bukatar daukan karin wasu matakan na daban da ya kamata.

Ministan tsaron na Jamhuriyar Nijar wanda ya jaddada bukatar goyon bayan al’umma a yakin da a ke gwabzawa da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ya nuna rashin jin dadinsa game da yadda wasu motocin yakin da kasar ta yi oda ke tsare a tashar ruwan Cotonou kamar yadda wasu kasashen yammaci da bai ambaci sunayensu ba suka rike jiragen yakin da kasar ta cefano.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Nijar, Burkina Faso, Mali Sun Daura Damarar Yaki Da Ta'addanci. MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG