Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uwargidan Shugaban Amurka Jill Biden Ta Kamu Da COVID-19

Shugaban kasar Amurka Joe Biden da matarsa Jill Biden
Shugaban kasar Amurka Joe Biden da matarsa Jill Biden

Uwargidan shugaban Amurka Jill Biden ta kamu da cutar COVID-19 kuma a halin yanzu tana fama da alamu masu sassauci, in ji Fadar White House a ranar Litinin.

WASHINGTON, D.C. - An kuma yi wa Shugaba Joe Biden gwajin na COVID-19 a yammacin ranar Litinin amma bai kamu da cutar ba, kamar yadda fadar ta White House ta fada cikin wata sanarwa.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden da matarsa Jill Biden Lokacin da suke barin gida
Shugaban kasar Amurka Joe Biden da matarsa Jill Biden Lokacin da suke barin gida

"A yammacin jiya Litinin ne, a wani gwaji da aka yi ya nuna cewa uwargidan Shugaban kasar ta kamu da COVID-19," in ji darektan sadarwar ta, Elizabeth Alexander, a cikin wata sanarwa.

"Za ta zauna a gidansu da ke Rehoboth Beach, a jihar Delaware." Sanarwar ta kara da cewa. .

Shugaban kasar Amurka Joe Biden da matarsa Jill Biden Lokacin da suke sauka a jirgi zuwa hutu
Shugaban kasar Amurka Joe Biden da matarsa Jill Biden Lokacin da suke sauka a jirgi zuwa hutu

Biden ya dawo Delaware shi kadai a yammacin Litinin ba tare da uwargidansa ba.

"Bayan gwajin da aka yi wa uwargidan shugaban kasa na COVID-19 da ya nuna ta kamu da cutar ne ya sa a gaggauta yi wa Shugaba Biden gwajin na COVID duka a yammacin Litinin," in ji Fadar White House. "Gwajin ya nuna Shugaban bai kamu da cutar ba, amma za a yi wa Shugaban gwaji akai-akai a wannan makon kuma za a sa ido kan alamun."

Shugaban kasar Amurka Joe Biden da matarsa Jill Biden Lokacin da suka isa Delaware hutu
Shugaban kasar Amurka Joe Biden da matarsa Jill Biden Lokacin da suka isa Delaware hutu

Fadar White ba ta ce uffan ba, bayan da aka nemi ta yi karin bayani kan ko wannan lamari zai shafi tafiyar da za yi zuwa ketare.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG