Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Wani Sabon Nau’in Covid-19 a Afirka Ta Kudu  


Masana kimiyya a Afirka ta Kudu sun ce sun gano sabon nau'in COVID-19.

Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Ƙasa ta sanar jiya Litinin a cikin wani sabon binciken ta bayyana cewa an fara gano irin wannan nau'in, wanda aka sanya wa suna C.1.2, a Afirka ta Kudu a watan Mayu na wannan shekarar, kuma tun daga lokacin ya bazu zuwa wasu ƙasashe bakwai na Afirka, Asiya, Turai da yankin kudancin Pacific na Oceania.

Masana kimiyya sun ce nau’in C.1.2 ya bayyana yana da halayya iri ɗaya da na wasu nau’in masu mamaye jiki baki daya inda suke cin nasarar karya karfin garkuwar jikin mutum.

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Amurka ta fada a ranar Litinin cewa alluran COVID-19 guda uku da ake amfani da su a yanzu a Amurka na ci gaba da tasiri sosai wajen hana kamuwa da cututtuka masu tsanani. Dokta Sara Oliver, masaniyar kimiyyar CDC, ta gaya wa kwamitin ba da shawara kan allurar rigakafin cewa allurar COVID-19 tana da tasiri karfin kashi 94 cikin dari wajen hana kwanciyar asibiti ga manya tsakanin shekarun 18 zuwa 74 daga watan Afrilu zuwa Yuli, lokacin da nai’in delta ya zama mafi rinjaye.

Dokta Oliver ta shaida wa kwamitin cewa alluran rigakafin ba su da tasiri sosai wajen hana kamuwa da cuta ko rashin lafiya,saboda nau’in Delta ya raunata karfin allurar bayan an ja tsawon lokaci.

Kwamitin mai ba da shawara na duba ko zai ba da shawarar ba da izinin karin allura na uku na rigakafin Pfizer, Moderna ko Johnson & Johnson a yayin da ake samun sabbin cututtukan COVID-19 a duk faɗin Amurka. Gwamnatin Biden kwanan nan ta ba da sanarwar za ta fara bayar da allurar rigakafin Pfizer ko Moderna karo na uku cikin wata mai zuwa. Dukansu CDC da Hukumar Abinci da Magunguna kwanan nan sun ba da shawarar allura karo na uku na Pfizer ko Moderna ga wasu mutanen da ke da raunin tsarin garkuwar jiki.

A wani ci gaba na daban ranar Litinin, CDC ta kara sabbin jerin kasashe bakwai mafi haɗarin balaguro saboda tsananin yaduwar COVID-19.

Azerbaijan, Estonia, Guam, Macedonia ta Arewa, yankin Amurka na Puerto Rico, tsibirin Caribbean na Saint Lucia da Switzerland an sanya su a matsayin Mataki na 4, wanda ke nuna haɗarin kamuwa da COVID-19. CDC ta ce yakamata mutane su guji yin balaguro zuwa waɗannan wuraren, kuma tana ba da shawara cewa duk wanda ya zama dole ne ya yi balaguro zuwa waɗannan wuraren yana buƙatar samun cikakkiyar allurar rigakafi.

XS
SM
MD
LG