Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Zai Yi wa Amurkawa Jawabi Kan Yadda Za A Tunkari Nau’in Omicron


Shugaban Amurka Joe Biden a Orangeburg, S.C.
Shugaban Amurka Joe Biden a Orangeburg, S.C.

Hauhawar adadin masu kamuwa da cutar a Amurka ya sa wasu jami’o’i da dama sun ayyana shirinsu na yin karatu daga gida, cikinsu har da Jami’ar Havard. 

Rahotanni daga sassan duniya na nuni da cewa cutar COVID-19 na ci gaba da karuwa.

A ranar Talata shugaban Amurka Joe Biden zai yi jawabi ga Amurkawa don bayyana yadda gwamnatinsa take shirin tunkarar annobar wacce take karuwa sanadiyyar wannan nau’in cutar.

Hauhawar adadin masu kamuwa da cutar a kasar ya sa wasu jami’o’i da dama sun ayyana shirinsu na yin karatun daga gida, cikinsu har da Jami’ar Havard.

Havard ta ce za ta kwashe makonnin ukun farko na watan Janairu tana karatu daga gida. A nahiyar turai, karin adadin masu dauke da cutar ya sa gwamnatoci suna kiran takaita wasu ayyuka.

Afirka ta Kudu ita ta fara ganin nau’in cutar na Omicron, a kuma ranar Juma’a ta ce za ta ba da gudunmowar allurai miliyan 2 na Johnson and Johnson ga wasu kasashe Afirka karkashin wani shirin da kungiyar tarayyar Afirka na AU Ke jagoarnta.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG