Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Gaza Samun Takardar Lamunin Daukaka Kara Ta Dala Miliyan 454 A Shari'ar Da Yake Fuskanta Kan Zamba - Lauyoyinsa


Donald Trump
Donald Trump

A yau Litinin Donald Trump ya gaza samun takardar shaidar da za ta ba shi damar daukaka kara kan hukuncin dala miliyan 454 da aka yanke wa tsohon shugaban na Amurka a wani zambar a birnin New York ba tare da damar tura kudin da kansa ba, a cewar lauyoyinsa.

WASHINGTON, D. C. - Wajibi ne Trump ko dai ya nemo kudin ko kuma ya tura takardar lamuni domin hana hukumomi kwace kaddarorinsa a yayin da yake kokarin daukaka kara akan hukuncin da mai shari'a Arthur Engoron ya yanke a ranar 16 ga watan Fabrairu da ya gabata inda ya umarce shi da wadanda ake kararsu su biya dala miliyan 464 a matsayin tara da kudin ruwa akan kadarorin da aka zuzuta darajarsu domin yaudarar bankuna da kamfanonin inshore.

A cikin karar da aka shigar a gaban kotu a ranar Litinin, lauyoyin na ‘dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican sun bukaci wata kotun ta jihar da ta jinkirta aiwatar da hukuncin, suna masu cewa adadin ya wuce gona da iri.

Sun kara da cewar, wanda ake karar ya tuntubi kamfanonin inshora 30 ta hanun wakilai daban-daban guda 4 domin samun takardar lamunin.

Lauyoyin Trump sun rubuta "Tabbatar da bukatu mai yuwuwa a matsayin sharadin daukaka kara zai haifar da raunin da ba za a iya gyarawa ba a kan wadanda ake tuhuma."

Lauyoyin sun nemi a maimakon haka a bar shi ya saka dala miliyan 100 yayin da yake daukaka karar hukuncin. Kamfanin haɗin gwiwa zai kasance a kan ƙugiya don kowane biyan kuɗi idan Trump ya rasa ƙararsa kuma ya tabbatar da cewa ba zai iya biya ba.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG