Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ci Trump Tarar Dala Miliyan 354.9 A New York


Tsohon Shugaba Donald Trump
Tsohon Shugaba Donald Trump

A wani hukuncin da ake ganin ya na iya lahani ga harkokin kasuwancin tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, an ci shi tarar kudi mai yawa a birnin New York baya ga takunkumin kasuwanci da aka kakaba ma shi.

Jiya Jumma’a, wani alkali a New York, ya zartas da hukunci cewa, dole tsohon Shugaban Amurka Donald Trump, ya biya tarar dala miliyan dari uku da hamsin da hudu, da dubu dari tara (354.9), wanda hakan wani koma baya ne ga tsohon Shugaban na Amurka, wanda wannan shari’a ke barazana ga harkarsa ta gine gine.

Baya ga tarar, an kuma dakatar da shi daga duk wata harkar kasuwanci a New York na tsawon shekaru uku.

Alkali Arthur Engoron ya kuma haramta ma Trump zama wani jami’i ko darakta, na kowani irin kamfani ne a New York, na tsawon shekaru uku.

A karar, wadda Attoni Janar ta New York Letitia James ta gabatar, an tuhumi kamfanonin Trump da iyalinsa da laifin shara karya wajen bayyana dukiyarsu, da karin dala biliyan 3.6 a shekara guda har na tsawon shekaru 10 saboda su yaudari bankuna su ba su basuka bisa sharudda masu sauki.

Lauyar da ke kare Trump, Alina Habba, ta ce, “Wannan ba kan Trump kawai zai tsaya ba – muddun aka bar wannan hukuncin a haka, zai zama wata alama ga kowane Ba’amurke cewa birnin New York ya daina zama wurin kasuwanci.” Ta ce za su daukaka kara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG