Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Da Biden Sun Lashe Zabubbukan Fidda Gwanin Gagarumar Talata Ta “Super Tuesday”


Trump Da Biden
Trump Da Biden

Shugaban Amurka Joe Biden da tsohon Shugaban Kasar Donald Trump na daf da samun tikitin yiwa jam’iyyunsu na Democrats da Republican takara.

Donald Trump ya samu nasara a jihohi 14 da suka gudanar da zabubbukan fidda gwaninsu a ranar “Gagarumar Talatar”, ciki harda Texas da California saidai ya fadi warwas a zaben jihar Vermont inda Nikki Haley ta bada mamaki.

Tsohon Shugaban Kasar, wanda fafutukarsa ta komawa fadar White House ke daukar hankali bayan daya sha kaye a hannun Joe Biden na jam’iyyar Democrats a shekarar 2020, ya samu goyon bayan dimbin wakilai a Talatar data gabata a kokarinsa na samun tikitin yiwa jam’iyyarsa ta Republican takara.

Ana yiwa jihohi irinsu Alabama da Alaska da Arkansas da Colorado da California da Maine da Massachussets da Minnesota da North Carolina da Oklahoma da Tennessee da Texas da Utah harma da Virginia wuraren da Trump keda dimbin magoya baya, shima kuma ya bayyana godiya garesu a shafin sadarwassa na Truth Social.

Dadaddiyar abokiyar hamayyarsa, tsohuwar jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley, wacce ta samu nasara a zaben fidda gwanin jihar Vermont da dan karamin rinjaye. har yanzu taki janyewa daga takarar.

A zaben fidda gwanin jam’iyyar Democrats kuwa, kamar yadda aka zata, biden ya samu nasara a jihohi 15, duk da cewar yayi rashin nasara a hannun wani abokin hamayyarsa da bai shahara sossai ba Jason Palmer a yankin wani karamin tsibiri me suna American Samoa dake cikin tekun pacific.

Wata kididdigar jin ra’ayin jama’a me taken “ainihin siyasar a bayyanai” ko realclearpolitics a turance ta nuna cewar Trump nada tazarar maki 2 a farin jini akan biden a fafatawar mutum da mutum a zaben da zai gudana cikin watan Nuwamba me zuwa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG