Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yunkurin Soke Takarar Trump Ya Gamu Da Cikas A Kotun Kolin Amurka


A Alhamis din nan Alkalan Kotun Kolin Amurka suka tsinci kawunansu a wani hali na tababa dangane da hukunci akan batun haramtawa tsohon Shugaban Kasar Amurka, Donal Trump shiga zaben fidda gwanin jam'iyyarsa a jihar Colorado

Ana nema a hana tsohon Shugaban kasar tsayawa takara saboda rawar daya taka yayin wani bore daya kai ga kaiwa Majalisar Dokokin Kasar ta Capitol hari a shekarar 2021, a wata shari'a mai tasirin gaske ga zaben Shugaban kasar da zai gudana a ranar 5 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Alkalan Kotun tara (9) sun tafka mahawara akan karar da Shugaba Trump ya daukaka akan hukuncin babbar kotun jihar Colorado na ranar 19 ga watan Disambar bara na yunkurin hana shi shiga zaben fidda gwanin jam'iyyarsa ta Republican a jihar ta hanyar amfani da Kundin Tsarin Mulkin Amurka na 14 da aka yiwa kwaskwarima, bayan samunsa da hannu a boren da aka yi.

Sashe na 3 na kundin da aka yiwa kwaskwarima "ya haramtawa duk wani jami'in gwamnatin Amurka daya taba yin rantsuwar kare martabar kundin daga bisani kuma aka same shi da hannu a bore ko yiwa kundin tawaye ko kuma taimakawa ko tallafawa makiyan kasa sake rike wani mukamin gwamnati.

aAkalan sun shafe tsawon lokaci suna muhawara akan yadda ya dace kasa ta aiwatar da sashe na 3 na kundin tsarin mulkin Amurka akan 'yan takara, musammanma wajen maida hankali akan cewar sai an jira majalisa ta fara yin doka akan batun.

Alkalan, masu ra'ayin rikau da masu ra'ayin gaba dai-gaba dai sun bayyana damuwa akan jihohi su samu ikon da zai yi tasiri na kai tsaye akan zaben shugaban kasar na gama-gari.

Masu adawa da Trump sun bukaci a hana masa takara a fiye da jihohin kasar 24, yunkurin da bai yi nasara ba, sakamakon rawar daya taka a harin da aka kaiwa ginin majalisar Capitol a ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2021.

Jihar Maine ma ta haramta masa shiga zaben fidda gwanin, hukuncin da aka jingine har sai an samu hukuncin Kotun Kolin akan shari'ar jihar Colorado.

An dai tsara gudanar da zaben fidda gwanin jam'iyyar Republican na jihar Colorado a ranar 5 ga watan Maris mai kamawa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG