Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta kama wasu magoya bayan jam’iyyar NNPP bisa zargin yunkurin ta da husuma.
Ana zargin Sharu Abubakar Tabula da Isma’il Iliyasu Mangu da laifin yada wani bidiyo da suka nada a lokuta daban-daban a shafukan sada zumunta, wadanda za su iya ta da husuma a cewar DSS.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kakakin hukumar ta DSS Peter Afunanya ne ya tabbatar da kama mutanen biyu a ranar Alhamis.
Hukumar ta DSS ta ce ba za ta zura ido tana kallo wasu suna kokarin ta da husuma a jihar ta Kano ba.
A kwanakin baya rundunar ‘yan sandan jihar ta Kano ta yi gargadi ga wadanda suke kokarin ta da hatsaniya a lokacin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha da za a yi ranar Asabar.
Gargadin na zuwa ne bayan da ta ce bincikenta ya gano wasu na shirin ta da zaune tsaye a lokacin zaben.
Jam’iyyu da dama ne za su fafata a zaben na gwamna a jihar ta Kano, amma hammaya ta fi zafi tsakanin APC mai mulki ta Gwamna Umar Abdullahi Ganduje da kuma NNPP ta tsohon Gwamna Dr. Rabiu Kwankwaso.
Jam'iyyar ta NNPP a martanin da ta mayar, ta zargi hukumar ta DSS da hada kai da jam'iyya mai mulki don cimma wata manufar siyasa.