Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar DSS Ta Bankado Yunkurin Kafa Gwamnatin Rikon Kwarya a Najeriya Sabanin Doka


Jami'an DSS a Najeriya (AP)
Jami'an DSS a Najeriya (AP)

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS ta tabbatar da yunkurin da wasu ke yi domin samar da gwamnatin rikon kwarya a Najeriya, hukumar ta ce ta na ganin hakan ba wai kawai a matsayin katobara ba ce, amma wani shiri ne na yi wa tsarin demokradiyya kafar ungulu da kuma son jefa kasar cikin rikici.

Wata sanarwa da huumar DSS ta aiko wa Sashin Hausa na Muryar Amurka, mai dauke da sa hannun kakakinta Dr. Peter Afunyaya, ta ce tabbas ba za a amince da yunkurin ba cikin tsari irin na demokradiyya da ke zuwa bayan kammala zabuka cikin lumana a akasarin yankunan kasar.

DSS ta gano wadanda ke kitsa wannan ajandar sun gudanar da taruka da dama, inda a karshe suka cimma daukar nauyin tayar da tarzoma wacce za ta haddasa zanga zanga a manyan biranen kasar, da hakan zai ba su damar samun ganin an ayyana dokar ta baci kana sai su rankaya kotu don samun hukuncin hana kaddamar da sabbin gwamnatoci a matakan tarayya da jihohi.

Saboda haka, hukumar DSS ta ce tana tare da babban kwamandan askarawan kasar a kudirinsa na tabbatar da an sami sauyin gwamnati cikin lumana bisa doron doka, inda ta ce za ta hada kai da sauran hukumomin tsaro wajen ganin an sami nasarar mika mulki cikin lumana.

Hukumar DSS ta yi gargadi ga duk masu gigin ganin sun barar da tsarin demokradiyya da su yi wa kansu kiyamullaili su kuma shafa wa kansu ruwa su daina wannan mummunar aniyar ta su in ba haka ba kuma, to lallai za su yaba wa aya zaki.

DSS ta ja hankalkin masu ruwa da tsaki a bangaren shari'a da kafafen sadarwa da kuma kungiyoyin fararen hula da su yi kaffa-kaffa da taka-tsantsan don kar ai amfani da su wajen hargitsa kasa.

XS
SM
MD
LG