Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Na Binciken Gwamna Matawalle Na Zamfara Kan Zargin Badakalar Biliyan 70


Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC
Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta ce tana gudanar da bincike kan Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, kan zargin badakalar Naira biliyan N70B.

WASHINGTON, D.C. - Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ne ya sanar da haka a wani taron manema labarai a ranar Alhamis, inda ya ce hukumar na tsare da tsohon Ministan Wutar Lantarki, Sale Mamman, kan badakalar Naira biliyan N22B.

Bawa ya sanar cewa EFCC na binciken Gwamna Matawalle ne, kwanaki kadan bayan gwamnan ya bukaci hukumar da ta daina matsa wa gwamnoni da bincike ta mayar da hankali kan ministoci da jami’an fadar shugaban kasa.

Sai dai Bawa, wanda ya yi magana ta bakin Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar, Osita Nwajah, ya bayyana cewa bai kamata hukumar ta kula Matawale ta hanyar mayar da martani ba, amma ta yi hakan ne don ta tauna tsakuwa.

Amma a martanin, Bawa ya bayyana cewa hukumar na binciken mutane daga kowane bangare da kuma matsayi.

A cewarsa, abin da zai sa mutum ya fada komar hukumar shi ne aikata almundhana, kuma Matawalle ba shi da hurumin da zai zaba wa hukumar mutanen da za ta yi bincike a kansu.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa gwamnatin tarayya na cewa Gwamna Matawalle yana da ’yancin fadin ra’ayinsa na neman hukumar EFCC ta binciki jami’an da yake ganin suna cin rashawa a Fadar Shugaban Kasa da kuma ministoci masu barin gado.

Gwamna Matawalle a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce, “Ina so shugaban EFCC ya yi irin wannan gayyata ga jami’an Fadar Shugaban Kasa da kuma mambobin majalisar zartarwa ta tarayya, wadda ita ce mafi girman matakin gwamnati a kasar nan.”

Sai dai gwamnatin tarayya a martaninta ta bakin Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ta ce gwamnan ya bayyana ra’ayinsa ne, na kashin kansa.

A Najeriya dai gwamnonin da mataimakansu na da rigar kariya daga kama su ko gurfanar da su a gaban shari’a, yayin da suke kan karagar mulki, wanda wannan dalilin ne yasa hukumar EFCC ba ta kama Gwamna Matawalle ba.

Matawalle, wanda ya sha kaye a neman sake zabensa gwaman karon na biyu a zaben 2023 a watan Maris da ya gabata, zai kammala wa’adinsa na shekara hudu a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

XS
SM
MD
LG