Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Human Rights Watch Ta Nuna Damuwa Kan Halin Da Bazoum Ke Ciki


Mohamed Bazoum (AP)
Mohamed Bazoum (AP)

Kiran na Human Rights Watch na zuwa ne kwana guda bayan wani taro da kungiyar kasashen yankin yammaci Afirka ta ECOWAS ta yi a Abuja don neman yadda za a shawo kan rikicin na Nijar.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch, ta yi kira ga sajojin da suka yi juyin mulki a Nijar, da su tabbata Shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa da sauran mutanen da suke tsare da su, suna cikin koshin lafiya.

Kungiyar ta kuma kalubalanci dakarun juyin mulkin, da su nunawa duniya cewa suna mutunta hakkokin bil adama ta hanyar sakin wadanda suke tsare da su da kuma mayar da kasar ta Nijar ga hannun farar hula.

Kiran na Human Rights Watch na zuwa ne kwana guda bayan wani taro da kungiyar kasashen yankin yammaci Afirka ta ECOWAS ta yi a Abuja don neman yadda za a shawo kan rikicin na Nijar.

“Ni a nawa tunanin, rike Shugaba Bazoum a matsayin garkuwa, aiki ne na ta’addanci.” Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya fadawa manema labarai bayan taron na ranar Alhamis.

Dakarun da ke tsaron fadar shugaban kasar ta Nijar, sun tsare Bazoum a gidansa tun a ranar 26 ga watan Yulin da suka karbe mulki.

Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce, ta gana da Bazoum, da likitansa da kuma lauyansa da wasu makusantansa a ranar Alhamis a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

Sai dai kungiyar ta ce irin yanayin da ake tsare da shi ya sabawa ka'idojin mutunta dan adam tana mai cewa tun a ranar 2 ga watan Agusta aka katse wutar lantarkinsa sannan rabonsa da ya ga wani tun a ranar 4 ga watan Agustan.

Bazoum ya ce ba a barin shi ya yi magana da iyalansa da ke kawo masa abinci da sauran abubuwan bukata, sannan an hana dansa, wanda ke fama da lalurar zuciya ganin likitansa.

Bayan kammala taronta a Abuja, kungiyar ta ECOWAS ta ce har yanzu tana kan bakarta ta yin amfani da matakin soji wanda za ta dauka a matsayin zabi na karshe.

Rahotanni sun ruwaito cewa dakarun na Nijar, sun yi barazanar kashe Bazoum idan har aka kai musu farmaki.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG