Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Nijar Sun Rage Kudaden Awon Motocin Gwanjo


Shugaban Nijar, Bazoum Mohamed (Instagram/PNDS Tarayya)
Shugaban Nijar, Bazoum Mohamed (Instagram/PNDS Tarayya)

Hukumomin jamhuriyar Nijer sun bada sanarwar rage kudaden awon motocin da ake shigorwa kasar daga turai da nufin ba jama’a damar sayen motoci masu karancin shekaru yayinda a wani bangare matakin ke hangen bunkasa kasuwancin motoci.

Tsadar awon motocin gwanjo dake shiga Nijar daga kasashen turai wani abu ne da aka jima ana korafi akansa lamarin da ya sa jama’a suka fi maida hankali wajen sayen motocin da suka dade ana amfani da su don kaucewa biyan makudan kudaden awon Doune

Hakan ne mafari da gwamnatin kasar ta dauki matakin rangwame ga wadanda suka shigo da motocin da ba su fice shekaru 10 da soma zirga-zirga ba kamar yadda mataimakin babban darektan hukumar Douane colonel Abou Oubandaouaki ya bayyanawa a yayin taron manema labaran da ya kira.

Kungiyar masu sayarda motocin tourist a cewar kakakinta Alhaji Aminou Oumarou ta yaba da wannan mataki domin a cewarta abu ne da ko bayan habbaka harkokin kasuwanci zai bai gwamnatin damar samun kudaden shiga ta hanyar awo da biyan haraji.

Tsadar awon motocin gwanjo a Nijar wata matsala ce da ta sa masu fafitikar kare mahalli ke korafi akanta saboda a cewarsu abu ne da ke gurbata yanayi da muhalli sakamakon yadda jama’a ke karkata wajen sayen tsofafin motoci masu fitar da turiri maras iyaka a maimakon sayen motoci dake da lafiyar injin.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Hukumomin Nijar Sun Rage Kudaden Awon Motocin Gwanjo
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00


XS
SM
MD
LG