Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takukmin ECOWAS Kan Mali Ka Iya Hana Shugabanni Halartar Jana’izan Boubacar Keita


Rasuwar tsohon shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita mako guda bayan takaddamar da ta kunno kai tsakanin ECOWAS da gwamnatin rikon kwaryar ta Mali ta janyo aza ayar tambaya dangane da makomar takunkumin da kungiyar ta kakabawa Mali.

Abin la’akari yanzu shine yiwuwar aika tawagar shugabanni don halartar jana’izar mutunen da suke matukar zumunci da shi a zamanin da yake kan karagar mulki.

Hambararren shugaban kasar na Mali ya rasu ne mako guda bayan da shugabanin kasashen kungiyar CEDEAO suka rufe iyakokin kasashen kungiyar da kasar Mali saboda zargin gwamnatinta da saba alkawarin shirya zabe lamarin da ya haifar da tsamin dangantaka a tsakanin kasashen yammacin Afrika da Mali.

Dalilin da ya sa masu bin diddigin al’amuran yau da kullum a jamhuriyar Nijar ke aza ayoyin tambaya game da yadda bangarorin biyu zasu tunkari wannan al’amari.

Dan shekaru 76 a duniya Ibrahim Boubacar Keita ya fuskanci juyin mulkin soja a 2020 bayan da ya shafe shekaru 7 akan karagar mulki sakamakon abinda sojojin Mali suka kira lalacewar sha’anin tsaro a kasar da ‘yan ta’adda suka mamaye arewacinta, a yayinda cin hanci da handamar dukiyar jama’a suka yi katutu.

Fiye da shekara guda bayan tumbuke shi daga kujerar shugabanci har yanzu an kasa gano bakin zaren warwaren rikicin siyasar kasar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:

Takukmin ECOWAS Kan Mali Ka Iya Hana Shugabanni Halartar Jana’izan Boubacar Keita
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:24 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG