Kungiyar ta bukaci a hau teburin tattaunawa duk da cewa ana shirin kakabawa kasar takunkumin karya tattalin arziki mai tsanani saboda gazawar shugabanninta wajen shirya zabe.
A farkon wannan watan ne kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ta kakabawa kasar Mali takunkumi mai tsauri bayan da gwamnatin sojan kasar da ta kwace mulki a shekarar 2020 ta yi watsi da shirin yin zabe a watan Fabrairu ta kuma ce za ta ci gaba da mulki a kasar har tsawon shekaru hudu.
Kungiyar EU ta ce za ta dauki irin nata matakan bisa ga na ECOWAS, ta yiwu a wannan watan na Janairu. Ko da yake, Emanuela Del Re, jakadiyar EU ta musamman a yankin Sahel, ta ce a bude kofa take domin tattaunawa.
A wata hira da yammacin ranar Litinin, Del Re ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa, "matsayin Tarayyar Turai zai yi karfi akan wasu kudurorin ba tare da rufe kofa ba baki daya.
Del Re ta kuma ce dole ne mu ci gaba da tattaunawa da Mali saboda ba ma son mu ware kasar, muna son ganin kasar Mali da za ta iya shawo kan wannan rikicin," in ji Del Re. Ta kara da cewa ta yi imanin cewa za a yi tattaunawar.
Bangarorin biyu dai ba su fito fili sun bayyana wani shirin tattaunawa ba. Da aka nemi jin martani daga bangaren gwamnatin Mali, mai magana da yawun gwamnatin ya ce hukumomi ma a shirye suke su tattauna.
Takunkumin karya tattalin arziki da na siyasa da aka sanya wa kasar dake yankin Sahel a yammacin Afirka kusan ya mayar da ita saniyar ware, tare da dakile mata hanyoyin kasuwanci.
-Reuters