Shugabannin yammacin Afrika suna taro yau asabar a Mali da zumar warware takaddamar shugabancin kasar Ivory Coast. Membobin kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ECOWAS, sun bukaci shugaban kasar mai ci yanzu Laurent Gbabgo ya yi murabus daga mukaminsa, tare da barazanar amfani da karfin soJa idan ya ci gaba da bijirewa. Mr. Gbagbo ya yi watsi da bukatun da aka gabatar na mika mulki ga Alassane Quattara, wanda kasashen duniya suka hakikanta cewa shine, ya lashe zaben shugaban kasa zagaye na biyu da aka gudanar cikin watan Nuwamba. Jiya jumma’a shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma ya bayyana cewa, yunkurin shawo kan rudamin siyasar kasar Ivory Coast ta wajen kira ga daya daga cikin shugabannin ya yi murabus bai cimma nasara ba. Bisa ga cewarshi, zabi ya rage ga kungiyar ECOWAS ta tsaida shawara kan matakin da zata dauka. Mr. Zuma ya bayyana haka ne bayan ganawa da takwaransa na kasar Uganda Yoweri Museveni daya daga cikin masu shiga tsakani na KTA dangane da rikicin siyasar Ivory Coast.
Shugabannin yammacin Afrika suna taron a Mali da zumar warware takaddamar shugabancin kasar Ivory Coast
Shugabannin yammacin Afrika suna taron a Mali da zumar warware takaddamar shugabancin kasar Ivory Coast