Magoya bayan Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo sun ce barazanar yin amfani da karfin soji wajen tunbuke Gbagbo din na daga cikin kurin matsa masa lamba ya mika ragamar iko ga wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a matsayin wanda ya ci zaben Shugaban kasar, tsohon Firayim Minista Alassane Ouattara. Mai magana da yawun Gbagbo Ahoua Don Mello yace shugabanin yankin sun san cewa ba su da hurumin tara sojoji don yakar gwamnati mai ci. Bisa ga cewarsa, sojojin kasashen waje izinin kai hari kan Ivory Coast. Ya kuma nemi sanin abinda shugabannin kasashen Yammacin Afirka zasu cimma ta wajen amfani da soji ko kuma kaddamar da yaki. Shima babban Hafsan Sojin Kasar Janar Philippe Mangou ya bayyana jiya Lahadi cewa sojoji ba za su taba yin watsi da Mr. Gbagbo ba. Yayinda suke cigaba da tattaunawa kan yiwuwar kai dauki a matakin yanki, shugabannin kasashen yammacin Afirka na ta daukar matakan kara maida Mr. Gbagbo saniyar ware ta fuskar tattalin arziki.
Magoya bayan Laurent Gbagbo sun ce kuri kungiyar hadin kan Afrika take yi da dace zata dauki matakin soji