Hukumar zabe ta kasar Uganda ta ce shugaba Yoweri Museveni ya lashe sabon wa’adi na shekaru 5 kan kujerar mulki, amma babban abokin adawar shugaban yayi fatali da wannan sakamako.
A yau lahadi hukumar ta bayyana cewa Mr. Museveni ya lashe zaben ranar jumma’a da kashi 68 cikin 100 na kuri’un da aka kada. Wanda ya zo na biyu, watau babban mai adawa da shi Kizza Besigye, ya samu kashi 26 cikin 100.
A cikin wata sanarwa a yau lahadi Mr. Besigye da jam’iyyu 4 dake kawance da shi sunyi watsi da sakamakon zaben, suka kuma ce duk wata gwamnatin da Mr. Museveni zai kafa haramtacciya ce. Mr. Besigye ya bayyana wannan sakamakon a zaman na bagu, ya kuma ce bai yarda da shugabancin Mr. Museveni ba.
Mr. Besigye dai shine tsohon likitan shugaban, kuma sau uku yana takarar kujerar shugabancin kasar da shi. Mr. Besigye yana shirin bayyana nasa sakamakon da ya tattara, ya kuma yi barazanar kiran jama’a da su fito kan tituna su yi zanga-zanga idan har adadin da hukumar zabe zata bayar bai yi daidai da nasa ba. Yayi gargadin cewa Uganda ta shirya domin gudanar da tunzuri irin wanda aka yi a kasar Masar.