Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’ai a Damokaradiyar jamhuriyar congo sun ce an kama wani babban jami’in soji sakamakon fyaden da aka yiwa mata da dama farkon wannan watan


Dakarun Majalisar Dinkin Duniya suna sintiri a kauyen Kimua, dake gabashin Congo. (File Photo)
Dakarun Majalisar Dinkin Duniya suna sintiri a kauyen Kimua, dake gabashin Congo. (File Photo)

Jami’ai a Damokaradiyar jamhuriyar congo sun ce an kama wani babban jami’in soji sakamakon fyaden da aka yiwa mata da dama farkon wannan.

Jami’ai a Damokaradiyar jamhuriyar congo sun ce an kama wani babban jami’in soji sakamakon fyaden da aka yiwa mata da dama farkon wannan watan. An kama Laftanar kanar Kibibi Mutwara ne a lardin Kivu dake kudancin kasar jiya jumma’a. Ana zargin Mutwara da umartar sojoji su yiwa sama da mata hamsin fyade a yankin Fizi dake gabashin Congo ranar jajibirin sabuwar shekara. Kakakin Majalisar Dinkin Duniya yace an kuma kafa wadansu sojoji goma jiya. Kanar Mutwara dai ya musanta hannu a fyaden. Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa, kimanin mutane dubu goma sha biyar ake yiwa fyade kowacce shekara a Congo ta Kinshasa. Ana kuma zargin dakarun gwamnatin da kungiyoyin ‘yan tawaye da aikata fyaden da kisan gilla da kuma wadansu miyagun laifuka.

XS
SM
MD
LG