Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’in Tarayyar Afirka mai shiga tsakani a rikicin Ivory Coast zai sake zuwa babban birnin kasar, Abidjan

Daliban kasar Ivory Coast suna zanga zanga kusa da wata motar Majalisar Dinkin Duniya da aka kona a birnin Abidjan, 13 Jan 2011

Jami’in Tarayyar Afirka mai shiga tsakani a rikicin Ivory Coast zai sake zuwa babban birnin kasar, Abidjan, bayan ganawa da shugaban kungiyar habaka tattalin arzikin Afirka ta yamma da tayi barazanar yin amfani da karfin soji don korar shugaba mai ci. Komawar Firayim Ministan Kenya Abidjan ta biyon tattaunawarsa a Nijeriya da shugaba Goodluck Jonathan, wanda ke shugabancin Kun giyar ta kasashen yammacin Afirka-ECOWAS. Wannan kungiyar ta ECOWAS dai na barazanar amfani da soji domin hambarar da shugaba mai ci Laurent Gbagbo karfi da yaji muddun ya ki mika ragamar iko ga wanda duniya ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben na watan Nuwamba, Alassane Ouattara. Mr. Ouattara dai ya gayawa Muryar Amurka cewa shi fa yana ganin Mr Gbagbo bai daku shiga tsakanin da kasa da kasa ke yi da wani muhimmanci ba. Bisa ga cewarsa, Mr. Gbabgo yana dabara ne kawai don ya ja lokaci.

XS
SM
MD
LG