Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ECOWAS Ta Kori Gwamnan Babban Bankinta

Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo yake ganawa da PM Kenya Ra'ila Odinga,wakilin AU mai shiga tsakani a rikicin siyasar kasar.
Shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo yake ganawa da PM Kenya Ra'ila Odinga,wakilin AU mai shiga tsakani a rikicin siyasar kasar.

Shugabannin kasashe dake yammacin Afirka sun tilastawa gwamnan babban bankin yankin,saboda ya ki daina baiwa Laurent Gbagbo kudi.

Shugabannin kasashe dake yammacin Afirka sun tilastawa gwamnan babban bankin yankin,saboda ya ki daina baiwa Laurent Gbagbo kudi.

Shugabannin kasashe dake yammacin Afirka da suke taro a Mali, jiya Asabar suka amince da murabus na gwamnan babban yankin,Phillip Dacoury-Tabley.Tabley yana goyon bayan Gbagbo,kuma ana zarginsa da ci gaba da baiwa Gbagbo kudi.

Babban Bankin yammacin Afirka ya amince da zaben abokin hamayyar Gbagbo, Alassane Ouattara,shugaban Ivory Coast,a zaben kasar da aka yi cikin watan Nuwamba, da har yanzu ake gardama akai.

Shugabannin kasashen ECOWAS sun bukaci Mr. Ouattara ya bada sunan mutunminda zai maye Mr.Tabley a matsayin Gwamnan babban bankin.

Mr.Gbagbo ya yi kunnen uwar shegu da bukatar da ake masa na mika mulki ga abokin hamayyarsa,mutuminda Duniya tace shine ya lashe zaben fidda gwanin.Cikas da aka samun ya janyo rikicin siyasa cikin kasar dake yammacin Afirka.

A wani lamari kuma jiya Asabar,gwamnatin Laurent Gbagbo,ta soke takardun jakadan Faransa a kasar,domin Faransar ta goyi bayan Alassane Ouattara a matsayin shugaban kasa.

Faransa tayi watsi da sanarwar, tana mai cewa bata da tasiri.Tuni Mr. Ouattara ya nada Ali Coulibaly, jakadan Ivory Coast a Faransa.

XS
SM
MD
LG