Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da umarnin da shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo ya baiwa jami’an ‘yansanda da sojojin kasar,da su binciki duk motocin majalisar dinkin Duniya.
Wani kakakin majalisar Martin Nesirky ya fada jiya jumma’a cewa, dokar ko kusa ba zata karbu ba,domin hakan ya keta matuka yarjejeniyar da aka tsaida wajen tura sojojin kiyaye zaman lafiya Ivory Coast.
Wani kakakin sojin kasar ne ya bayyana wan nan sabuwar dokar a tashar talabijin ta kasar,yana mai cewa an dauki matakin ne domin tabbatar da cewa sojojin Majalisar Dinkin Duniya basa hada baki da magoya bayan abokin mahayyar Mr. Gbagbo, Alassane Ouattara.
A baya Mr. Gbagbo ya umarci dokacin sojojin majalsiar su fice daga Ivory Coast,saboda yana zargin suna nuna son zuciya a rikicin kasar.
Majalisar dinkin Duniya ta yi watsi da umarnin,kuma a farkon makon nan ma ta bada sanarwar zata kara karfin sojojin kiyaye zaman lafiyar da dakaru dubu biyu, wanda zai kawo adadinsu zuwa dubu 12.