Shugaba John Atta Mills na Ghana ya ce kasarsa ba zata goyi bayan kowane bangare a rikicin siyasar kasar Ivory Coast ba, kuma zata goyi bayan kowace gwamnati ce ta ke kasar.
A lokacin da yake magana da 'yan jarida yau Jumma'a, Mr. Mills ya ce Ghana ba ta goyon bayan yin amfani da sojoji wajen kawar da shugaba Laurent Gbagbo dake kan gadon mulki daga karagarsa.
Da alamun wadannan kalamu na shugaban Ghana zasu nakkasa goyon bayan da Alassane Ouattara yake samu a yankin na yammacin Afirka. Akasarin kasashen duniya sun aminvce da Ouattara a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasa na watan Nuwamba a Ivory Coast.
Kungiyar tattalin Arzikin Yammacin Afirka ta ECOWAS ko CDEAO, ta yi barazanar yin amfani da karfin soja domin kawar da Mr. Gbagbo idan bai yarda ya mika mulki ga Ouattara ba.
A wani labarin kuma, kasashen Canada da Britaniya sun sa kafa sun shure korar jakadunsu da gwamnatin Mr. Gbagbo ta ce ta yi daga kasar Ivory Coast. Kasashen biyu sun ce Alasdsane Ouattara ne kawai yake da ikon yin haka a kasar Ivory Coast.