Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban Ki-moon Yana Aza Laifin Tarzomar Ivory Coast Kan Laurent Gbagbo


Local residents look on as a UN vehicle, set on fire by militant student supporters of Laurent Gbagbo, burns in the Riviera 2 neighborhood of Abidjan, 13 Jan 2011
Local residents look on as a UN vehicle, set on fire by militant student supporters of Laurent Gbagbo, burns in the Riviera 2 neighborhood of Abidjan, 13 Jan 2011

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya,Ban Ki-moon yace sami bayanan sirri da suka nuna cewa shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo dake tsaka mi wuya da mukarrabansa sune suke ingiza magoya bayansu su tada tarzoma.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya,Ban Ki-moon yace sami bayanan sirri da suka nuna cewa shugaban kasar Ivory Coast,Laurent Gbagbo,dake tsaka mi wuya da mukarrabansa ne suke zuga ingiza magoyabayansu su tada tarzoma.

Jiya jumma’a babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya ya gayawa manema labarai cewa ya damu ainun kan karuwar tashe tashen hankula a Ivory Coast da ake aunawa kan farar hula da kuma sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar Dinkin Duniya,sakamakon gardamar da ta biyo bayan zaben kasar cikin watan Nuwamba.

Yace yana da bayanai masu sahihanci kan keta hakkin buil’adama cikin kasar,daga nan yace masu tada tarzoma su yi kuka da kansu.

Babban magatakardan yace abin takaici ne ganin Mr.Gbagbo yaki ya mutunta muradin al’umar kasar.

Tunda farko a jiya jumma’an,babban kwamishinan kula da hakkin bil’adama na Majalisar, Rupert Colville,yace an kashe akalla mutane metan 47 a tarzomar da ta biyo bayan zaben a Ivory Coast.

XS
SM
MD
LG