Majalisar Dinkin Duniya tace tana bukatar Karin sojoji dubu daya zuwa dubu biyu a Ivory Coast a lokcind aake ci gaba da rikicin siyasa da ya biyo baytan zaben kasar, ganin shugaban kasar mai ci yaki ya mika mulki.
Jagoran ayyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Ivory Coast, Alain Le Roy, ya fada jiya laraba cewa ofishinsa zai gabatarwa kwamitin sulhu wan nan bukata,da burin za’a tura karin dakarun cikin makonni masu zuwa. Sojojin kiyaye zamen lafiya ne suke bada kariya ga O’tel din da Alassane Ouattara,mutuminda duk Duniya ta amince shine ya lashe zabe, yake zaune ciki tun bayan kammala zaben.
Kuma Majalisar Dinkin Duniya tace fiyeda mutane 170 ne aka kashe a tarzoma da ta barke bayan zaben da aka yi cikin watan Nuwamba. Duk da kokarin da shugabannin kasashen Afirka suka yi na kawo karshen rikicin da alamun hakan ya ci tura.
Ranar Talata kungiyar ECOWAS tace shugaba Laurent Gbagbo ya yi alkawarin kawo karshen killacewar da dakarun Majalisar Dinkin Duniya suka yi wa O’tel da Alassane Ouattara yake ciki.
Duk da haka shaidu sun bada labarin cewa har yanzu shingaye da aka kafa kan hanyoyin zuwa O’tel din dake birnin Abidjan suna nan,kuma sojoji suna ci gaba da mai da motoci dake kokarin tunkarar wurin.
Jiya laraban,babban jami’in difilomasiyyar Amurka mai kula da shiyyar Afirka Johnnie Carson, yace har yanzu Gbagbo yana iya amsa tayin barin mulki cikin mutunci da kuma samun mafaka da aka bashi.Duk da haka yace, Amurka ta hakikance cewa tilas ne Gbagbo ya mika mulki ga mutuminda ya sami nasara a zaben.
Da yake magana kan barazanar amfani da karfin soji da ECOWAS ta yi, wani babban jami’in kungiyar Mr.James Gbeho,yace shugabannin kungiyar sun san irin matsaloli dake tattare da aiwatar da shirin,duk da haka yace ba zasu yi wata wata ba wajen amfani da karfin tsiya idan aka kasa warware rikicin cikin ruwan sanyi.