Yau lahadi ce ‘yan kudancin Sudan suke kada kuri’a da zata shiga tarihi kan ‘yancin kai,zaben zai baiwa mazauna yankin zabin ci gaba da zama cikin Sudan ko su balle su kafa kasa mai cin gashin kai.
Ana kyautata zaton yankin zai kada kuri’ar ballewa. Shugaban yankin kudancin Sudan Salva Kiir ya kira kuri’ar abin tarihi ga al’umarsa.
Dubban yan Sudan ne suka shiga layi tun cikin dare domin su kasance daga cikin mutanen farko da zasu kada kuri’arsu.
Kusan mutane milyan hudu ne suka yi rijista domin zaben,wadda yana daga cikin sharadin yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a 2005,wacce ta kawo karshen yakin basasar kasar.
Manyan mutane daga sassan Duniya daban daban ciki har da tsohon shugaban kasar Amurka Jimmy carter,da tsohon babban sakaten Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan,da tsohon shugaban Afirka ta kudu duk sun isa yankin.
Ahalin yanzu kuma an kashe akalla mutane tara a gwabzawar da ‘yan tawayen kasar suka suka yi sojojin SPLA na kudancin Sudan a karshen mako.