An kasha ‘yansanda akalla biyar a kasar Ivory Coast inda aka sake daukar-ba-dadi tsakanin magoya bayan hinjararren shugaban kasar Laurent Gabgbo da na Alassane Ouattara, wanda suke jayayyar ragamar mulki da juna.
‘Yansanda da kuma shaidu duk sunce wannan fadan na yau anyi shine a gundumar Abobo inda a nan ne a jiya ma aka gwabza a tsakaninsu, har aka hallaka wasu mutane biyar fararen hula.
Wannan gundumar ta magoya bayan Alassane Ouattara ce, mutumin da duk kasashen duniya suke runguma akan wanda ya lashe zaben shugaban kasan da aka yi.
Laurent Gabgbo, wanda soja ke ci gaba da yiwa biyayya, dai yana ci gaba da kin mika ragamar mulki duk kuwa da matsin lambar da yake sha daga wurin kasashen duniya. Kuma har yanzu shi Mr. Ouattara yana ci gaba da zama a cikin wani otel a karkashin kariyar sojan Majalisar Dinkin Duniya.
A cikin makon nan ne ake sa ran cewa Pirayim Ministan Kenya Oginga Odinga zai sake dawowa Abidjan, zuwansa na biyu, na kokarin ganin cewa an warware wannan rikicin siyasar na Cote d’Ivoire cikin lumana.