Asabar ministan tsaron Faransa ya gaskanta rahoton dake cewa an kashe ‘yan kasar Faransan nan biyu,kwana guda bayan da aka kama su a wata maciyar abinci a birnin Niamey babban birnin Nijar.
Sun rasa ransu ne a lokacin da ake kokarin ceto su.
Cikin wata sanarwa, minister Juppe yace sojojin Nijar tare da taimakon sojojin Faransa dake yankin sun bi sawun wadanda suke garkuwa da mutanen har zuwa kan iyakar Nijar da Mali,sun kashe da dama daga cikinsu.
Sanarwar ta kara da cewa a karshen matakin sojin ne aka gane gawar wadanda ake garkuwa dasu din. Babu bayanai nan take da suka bayyana yadda mutanen suka rasa ransu, amma kamfanin dillancin labaran Reuters ya ci daga bakin wani kakakin sojin Faransa dake cewa,Paris ta hakikance cewa masu garkuwa da mutanen ne suka kashe su.
Shugaban Faransa,Nicolas Sarkozy yayi Allah wadai dakisan,ya kira hakan dabbanci.
Zuwa yanzu dai babu wata kungiya ko mutum da ya fito ya dauki alhakin satar mutanen.