Jamian rundunar sojin kudancin Sudan sun ce a kashe a kalla mutane 4 a wata arangama tsakanin ‘yan tawaye da Sudan People’s Liberation Army, ‘yan sa’oi kafin fara kada kuri’ar raba gardama. Kanar Philip Aguer yace sojoji sun yi fito da mu gama da mayakan dake goyo bayan shugaban ‘yan tawaye Gatluak Gai a kudancin kasar. Babu tabbacin ko wadanda aka kashe sojojin rundunar bane ko kuma mayaka. An kai harin ne yayinda ake shirin kada kuri’ar raba gardama da zata ba kudancin Sudan zabi tsakanin ci gaba da kasancewa tare da sauran kasar ko kuma ballewa su kafa kasa mai cin gashin kai. Ana kyautata zaton yankin zai zabi samun ‘yancin kai. Kuri’ar da za a kada na tsawon mako guda, na daga cikin alkawuran da aka dauka, a yarjejeniyar zaman lafiya cikin shekara ta dubu biyu da biyar da ta kawo karshen yakin basasa tsakanin kudanci da arewacin kasar.
An kashe wadansu mutane hudu a kudancin Sudan a wata arangama