Daya daga cikin shugabannin kungiyar Zumunta ta 'yan arewacin Najeriya Mr. Danladi Suleiman ya bayyana farin cikin 'yan kungiyar da sauran 'yan Najeriya kan ziyarar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai fara anan Washington DC,a ranar wannan lahadi 19 ga watan Yuli.
Da yake bayyana haka a hira da Mahmud Lalo, Mr. Suleiman yace ziyarar zata yi fa'ida domin akwai alamun Amurka tana neman hadin kai da Najeriya saboda a taimaka mata musamman ta fuskar tsaro, ganin irin matsalar rashin zaman lafiya da Boko Haram ta haifar.
Mataimakin shugaban na Zumunta yace kungiyar a zaman kanta bata shirya wani abu ba domin zuwan shugaba Buhari, amma babbar kungiyar da take a zaman laima ga kungiyoyin 'yan Najeriya a Amurka mai lakabin NIDO, ta shirya taro da shugaba Buhari inda zai sadu da 'yan Najeriya, kuma ita ma zumunta da wakilanta zasu halarci wannan zama.
Suleiman yace gayyatar tana kuma iya zama rarrashi, saboda ganin yadda shugaba Obama ya kai ziyara wasu kasashen Afirka amma bai je Najeriya ba.
Shugaban na kungiyar zumunta ya bayyana farin cikin ganin yadda shugaba Buhari ya fara aiki domin 'yan Najeriya sun lura cewa shi ba mai wargi bane.
Ga karin bayani