Saboda rashin gane alkiblar 'yan Najeriya ko Najeriya kanta shugaban bai iya daukan matakan cika alkawuran da ya yi masu ba lokacin da yake fafutikar neman zabe.
Dalilin haka Muryar Amurka ta tambayi tsohon dan majalsar wakilai daga jam'iyyar APC wanda kuma yana kusa da Shugaba Buhari wato Barrister Ibrahim Bello yaya yake ganin APC zata iya warware dambarwar shugabanci tsakanin 'ya'yanta a majalisar dattawa.
Barrister Bello yace batun neman tsige mataimakin shugaban majalisar dattawa dan PDP mawuyacin hali ne yanzu. Yace duk wani ihu da hayaniya da jam'iyyarsu ke yi ba zasu cireshi ba sai dai idan shi yace ya bari ko kuma kashi biyu cikin uku na 'yan majalisar sun ce sun cireshi. Jam'iyya ba zata shiga majalisa tace zata yi hukunci ba saboda zabe ake yi. Babu yadda za'a yi dashi yanzu.
Dangane da ko su 'yan APC zasu hakura Barister Bello yace su basu yadda ba. Sakacin jam'iyyarsu ne da rashin hadin kan shugabanninsu da rashin yin abun da yakamata suka samu baraka har PDP ta samu kujerar mataimakin shugaban majalisar dattawa..
Shi kuma mukarrabin Shugaba Buhari Sahabi Sirika na ganin taka rawar da ta dace daga PDP alheri ne ga APC. Yace idan sun ci duk jihohi 36 zasu amsa amma jam'iyyar PDP kada ta ruguje. Ta kara karfi ta dinga sukarsu domin su yi abun da ya kamata.
Yanzu dai jam'iyyar APC ta kafa wani kwamitin sasanta rikicin majalisar dokokin a karkashin jagorancin gwmna Tambuwal. Amma wasu na tababan samun nasararsa.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.