Kotun sauraron kararrakin zabe ta fara sauraron shaidu dangane da karar da dan jam'iyyar PDP Injiniya Ahmed Mukhtar wanda yake kalubalantar dan majalisar wakilai ta tarayya Abubakar Lado, kan zargin dan majalisar bashi takardun shaidar kammala karatu na Firamare dana sakandare.
Lauyan mai kara Bala Tanko, ya gayawa wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari cewa sun gabatar da shaidu da suka hada da shugabar makarantar Firamare ko malama data karantar da Lado, da shugaban makarantar sakandare da kuma kamfanin madaba'ar buga takardu.
Amma a nasa gefen, dan majalisa Abubakar Lado, yace wannan yarfen siyasa ne kawai. Domin an ga cewa sun sami nasarar zabe kuma basu da gwamnati ake neman a yi musu ba dai dai ba.
Da aka tambayeshi baya shakkun zai sha kaye ganin shaidar da aka bayar daga malamansa da yake jefa ayar tambaya kan sahihancin takardun shaidar kammala karatun? Yace bayi da shakka.
Alkali Olatunde Oshodi ya tsaida 27 ga watan nan na 7 domin dan majalsa Abubakar lado da masu bashi kariya ya gabatar da shaidarsa.