Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shettima Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Duniya Kan Magance Matsalar ‘Yan Gudun Hijira


Kashim Shettima (Facebook/Bola Ahmed Tinubu Support Group Germany)
Kashim Shettima (Facebook/Bola Ahmed Tinubu Support Group Germany)

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya yi kira ga kawayen kasar da a hada kai domin magance matsalar ‘yan gudun hijira a kasar.

WASHINGTON, D. C. - Ya yi wannan kiran ne a yayin wani taron kaddamar da tsare-tsare na jihohi kan magance matsugunin cikin gida” wato “Launch of the State Action Plans on Durable Solution to Internal Displacement” da za a aiwatar a jihohin Arewa guda hudu da suka hada da Adamawa, Benue, Borno, da Yobe, wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa ta Villa a Abuja.

A wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai Stanley Nkwocha ya fitar, mataimakin shugaban kasar ya bayyana dabarun da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta dauka wajen tunkarar kalubalen ‘yan gudun hijira a Najeriya, inda ya ce al’ummar kasar na ba da fifiko ga rayuwar al’ummarta musamman a wannan mawuyacin lokaci.

Ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta himmatu wajen tabbatar da lafiyar da walwalar ‘yan gudun hijira a Najeriya.

Shirin ya samo asali ne daga maslaha ko dabarun da Babban Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya tsara kan ƙaura daga matsugunai wanda ke da nufin taimakawa mutanen da ke gudun hijira a cikin gida su sami mafita mai ɗorewa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG